An Kaddamar da Sabuwar Hukumar Hisbah Gandujiyya a Kano

An kaddamar da fom ɗin neman shiga kungiyar Hisbah Gandujiyya a ranar Asabar 6 ga Disamba 2025 a Kano, ƙarƙashin jagorancin jigon jam’iyyar APC, Hon. Baffa Babba Dan Agundi.
Taron ya samu halartar tsohon kwamandan Hisbah na jihar Kano, Sheikh Harun Ibn Sina, wanda ya jaddada muhimmancin samar da tsari mai inganci wajen kare tarbiyya da kyawawan ɗabi’u cikin al’umma.
Majiyar Arewa Update ta rawaito cewa ƙaddamarwar ta kasance mataki na farko na shirye-shiryen da kungiyar Hisbah Gandujiyya ke yi domin farfaɗo da ayyukan da ta bayyana cewa sun tsaya cik bayan korar daruruwan ma’aikata a baya.
Kungiyar ta sanar da cewa tana kan gyara manyan tsare-tsarenta da za su taimaka wajen tallafawa al’umma, musamman matasa da wadanda ke cikin halin rashin aiki a Kano.
A cewar kungiyar, kusan mutane dubu goma sha biyu da ta ce an kora daga Hisbah ta gwamnati a baya ne za su amfana da sabon tsarin da suka tanada.
Haka kuma an bayyana cewa kwamandojin sabuwar Hisbah daga kananan hukumomi 44 na jihar da wasu daga cikin jami’ansu ne suka halarci taron na ƙaddamarwar.
Hon. Dan Agundi ya bayyana cewa sabon tsarin zai mayar da hankali kan aiwatar da doka da oda cikin lumana, tare da nisantar da kungiyoyin matasa daga aikata miyagun laifuka.
Kungiyar ta Hisbah Gandujiyya ta sha alwashin yin aiki cikin gaskiya da adalci, tare da tabbatar da cewa sabbin matakan da za su aiwatar za su inganta zaman lafiya da tsaro a fadin jihar Kano.




