Blog

  • Hukumar Shari’ar Kano Ta Shawarci Iyaye Su Rinka Sanya ’Ya’yansu a Gaba Yayin Zuwa Sallar Tuhajjud

    Hukumar Shari’ar Kano Ta Shawarci Iyaye Su Rinka Sanya ’Ya’yansu a Gaba Yayin Zuwa Sallar Tuhajjud

    Hukumar Shari’a ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ta buƙaci iyaye da su rinƙa sanya ’ya’yansu a gaba, musamman ’yan mata, yayin da suke zuwa sallar dare ta Tuhajjud a wannan wata na Ramadan, domin kare su daga haɗuwa da wasu bata-gari da ka iya ɓata musu tarbiyya.

    Kwamishina na biyu na Hukumar Shari’ar Jihar Kano, Sheikh Ali Ɗan Abba, ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan da ya jagoranci saɓunta wasu kwamitocin hukumar guda biyu. Kwamitocin sun haɗa da Kwamitin Sulhu da kuma Kwamitin Tantance Limamai.

    An gudanar da taron saɓunta kwamitocin ne a ɗakin taro na hukumar da ke Kano.

    Sheikh Ali Ɗan Abba ya bayyana cewa sanya ’yan mata a gaba tare da iyayensu yayin zuwa masallaci domin halartar sallar Tuhajjud zai taimaka wajen kare su daga gurɓacewar tarbiyya.

    Ya kuma ƙara da cewa an saɓunta kwamitocin ne biyo bayan rushe tsoffin kwamitoci guda huɗu da suke a baya, inda aka haɗa su zuwa kwamitoci biyu domin ƙara inganta ayyukan addini da kuma ci gaban al’umma a sassan jihar.

    A yayin ƙaddamar da sabbin kwamitocin, Kwamishina na biyu Sheikh Ali Ɗan Abba ya kasance tare da Kwamishina na ɗaya, Gwani Hadi Ɗahiru Yakasai, da wasu daga cikin mambobin hukumar gudanarwa, da kuma mambobin sabbin kwamitocin.

  • Hukumar Shari’ar Kano Ta Shirya Shan Ruwa Tare da Sabbin tuba a Watan Ramadan

    Hukumar Shari’ar Kano Ta Shirya Shan Ruwa Tare da Sabbin tuba a Watan Ramadan

    Hukumar Shari’a ta jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ta gudanar da shan ruwa tare da waɗanda suka karɓi addinin Musulunci a Kano.

    Kwamishina na biyu a hukumar Shari’a ta jihar Kano, Sheikh Ali Ɗan Abba, ne ya jagoranci taron shan ruwan a harabar hukumar.

    Waɗanda suka musulunta, da manyan baƙi, haɗi da daraktoci da sauran shugabannin hukumar shari’ar da dama ne suka samu damar halartar taron shan ruwan.

    Da yake jawabi a yayin taron, Sheikh Ali Ɗan Abba, ya ce hukumar shari’ar, ta gudanar da shan ruwan tare da waɗanda suka musuluntar ne bisa sahalewar Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, inda ake shirya wa duk cikin watan azumin Ramadan, domin sanya musu farin ciki, a kuma yi addu’a ta musamman.

    A jawabinsa Wakilin Shugaban Kungiyar Taimakon Musulunci ta World Association of Muslim Youth WAMY, Malam Sunusi Ibrahim, ya bayyana cewar wannan tsari da ake yi abun a yaba ne tare da jinjinawa.

    A yayin taron shan ruwan, an kuma yi wa jihar Kano, da gwamnatin jihar ƙarkashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, addu’a, tare da ƙara samun zaman lafiya, da ci gaba mai ɗorewa a jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya.

  • DA ƊUMI ƊUMISA: Jami’an Tsaro Sun Kama Wanda Ake Zargi da Kashe Mata da ’Ya’yanta Guda Shida a Dorayi

    DA ƊUMI ƊUMISA: Jami’an Tsaro Sun Kama Wanda Ake Zargi da Kashe Mata da ’Ya’yanta Guda Shida a Dorayi

    Rahotanni da ke shigowa sun tabbatar da cewa jami’an tsaro sun kama wanda ake zargi da kashe wata mata tare da ’ya’yanta guda shida a unguwar Dorayi, da ke cikin birnin Kano.

    Wani mazaunin yankin, da ya nemi a sakaya sunan sa, ya shaida mana cewa an kama wanda ake zargin ne da misalin ƙarfe 2 na dare, bayan samun bayanan sirri tare da haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da mazauna unguwar.

    A cewar rahotannin da aka samu, kamen ya biyo bayan bincike mai zurfi kan wannan mummunan lamari da ya girgiza al’ummar Dorayi tare da jefa al’ummar jihar Kano cikin alhini da kaduwa.

    Mazauna yankin sun bayyana matuƙar jimami da tashin hankali bisa wannan lamari, inda suka yi kira ga hukumomi da su tabbatar da cikakken bincike mai zaman kansa, domin ganin an tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya shafa.

    Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayani a hukumance ba, sai dai sun tabbatar da cewa wanda ake zargi yana hannunsu kuma ana ci gaba da bincike domin gano hakikanin gaskiyar abin da ya faru.

    Za mu ci gaba da bibiyar wannan lamari tare da kawo muku ƙarin bayani da zarar an samu.

  • Khalid Yusuf Idris Ya Ajiye Aiki a Rahma TV, Ya Kaddamar da Sabuwar Kafar Zamani “KANO LIVE 24″

    Khalid Yusuf Idris Ya Ajiye Aiki a Rahma TV, Ya Kaddamar da Sabuwar Kafar Zamani “KANO LIVE 24″

    Shugaban Sashin Rahma TV da kuma Sashin Kafafen Sada Zumunta na tashar, Khalid Yusuf Idris, ya ajiye aikinsa a hukumance a tashar Rahma TV, domin mayar da hankali kan sabuwar kafar zamani da ya assasa mai suna KANO LIVE 24.

    Wani makusanci ga Khalid Yusuf Idris ne ya tabbatarwa Newshub24 wannan mataki, inda ya bayyana cewa shawarar ta biyo bayan dogon nazari, shawarwari da kuma burin samar da kafar yaɗa labarai ta zamani wadda za ta mayar da hankali kan sahihanci, sauri da kuma buƙatun al’umma a wannan zamani na fasaha.

    Majiyoyinmu sun nuna cewa Khalid Yusuf Idris ya shafe shekaru yana taka muhimmiyar rawa a Rahma TV, musamman wajen jagorantar sashen kafafen sada zumunta da kuma bunƙasa ayyukan tashar a duniyar zamani.

    A tsawon lokacin da ya yi a tashar, ya taimaka wajen inganta tsarin watsa labarai, haɓaka hulɗa da masu kallo da kuma isar da labarai cikin sauri da nagarta.

    A cewar majiyoyi, tafiyarsa daga Rahma TV ta gudana ne cikin mutunta juna da fahimta, inda bangarorin biyu suka yaba da irin gudunmawar da ya bayar a lokacin aikinsa, tare da yi masa fatan alheri a sabon babi na rayuwarsa ta sana’a.

    Sabuwar kafar KANO LIVE 24 na da burin zama sahihiyar majiyar labarai ta zamani, wadda za ta rika watsa labarai kai tsaye, rahotanni na musamman, shirye-shiryen tattaunawa, bayanai kan harkokin siyasa, zamantakewa, tsaro, tattalin arziki da kuma abubuwan da suka shafi rayuwar al’umma.

    Baya ga haka, kafar za ta yi amfani da hanyoyin zamani na kafafen sada zumunta domin kai wa jama’a labarai cikin gaggawa, tare da ba su damar yin mu’amala kai tsaye da shirye-shiryen da ake gabatarwa.

    Masana harkokin yaɗa labarai na ganin cewa ƙaddamar da KANO LIVE 24 zai ƙara faɗaɗa fagen yaɗa labarai a Jihar Kano da Arewa baki ɗaya, tare da samar da sabuwar dama ga matasa masu sha’awar aikin jarida da kafafen zamani.

    Ana sa ran kafar za ta fara aiki a hukumance nan ba da jimawa ba, inda za ta kawo sabbin tsare-tsare da dabaru domin biyan bukatun masu sauraro da masu kallo a wannan zamani.

  • Da ɗumi-ɗumi: Gwamna Abba Kabir Yusuf zai koma APC ranar Litinin

    Da ɗumi-ɗumi: Gwamna Abba Kabir Yusuf zai koma APC ranar Litinin

    Rahotanni daga DAILY NIGERIAN sun tabbatar da cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zai sauya sheƙa daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a hukumance ranar Litinin mai zuwa.

    Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa gwamnan ya riga ya isa Abuja domin kammala shirye-shiryen ficewarsa daga NNPP.

    Rahoton ya ce Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, tare da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Yitwalda Nentawe, ne za su karɓi gwamnan a birnin tarayya.

    Haka kuma, an tabbatar da cewa jagoran APC a Kano, Abdullahi Ganduje, an kira shi da gaggawa daga tafiyar da yake yi a Dubai.

    A gefe guda kuma, shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya rage zamansa a Umrah domin shirya ba gwamnan katin zama ɗan APC a Diso Ward, Karamar Hukumar Gwale a cikin makon nan.

    Idan hakan ta tabbata, Abba Kabir Yusuf zai zama gwamnan NNPP na ƙarshe da ya bar jam’iyyar, lamarin da ke ƙara ɗaga kura a fagen siyasar Kano da Arewa baki ɗaya.

  • Al’ummar Sabuwar Gandu Sun Yi Dafifi Wajen Walimar Kammala Aikin Alhaji Mukhtar Aliyu Custom

    Al’ummar Sabuwar Gandu Sun Yi Dafifi Wajen Walimar Kammala Aikin Alhaji Mukhtar Aliyu Custom

    Kafatanin Al’ummar Unguwar Sabuwar Gandu dake jihar Kano da makotansu sun yi fitar dango zuwa wajen walimar taya ɗan su, na Allah mutumin Allah, gwarzo abin koyi Alh Muktar Aliyu na kammala aikin da lafiya a hukumar Custom ta kasa.

    Taron ya gudanane a ranar Alhamis 1st January 2025, a dakin taro na Ali Jita Even Center dake kan titin Lawan Dambazau Road Kano, karkashin jagorancin Dr Ibrahim Muhammad Gandu, da Alh Anas tare da Abdullahi Abubakar Bisi da sauran yan kwamatin dattawan Sabuwar Gandu.

    Allah ya albarkaci taron da iyayen kasa hakimai da masu unguwanni da mutane masu dajara hadi da manyan abokanan aiki shi Alh Muktar din a gidan Custom da iyayen gidansa.

    An haifi Alhaji Mukhtar Aliyu a Gandun Sarki wato (Audu Bako Secretariat) ta yanzu a shekarar 1969. Ya fara neman iliminsa na addini tun yana dan shekara 3, a makarantar marigayi Malam Danyaro.

    A lokacin daya tasa ne aka saka shi a makarantar boko ta Gandun Nassarawa Primary School a shekarar 1977 zuwa 1982. Daga nan ne tafiya ta neman ilimi ta fara nisa, inda ya sami sa’ar shiga Karamar Sakandare ta Sabuwar Kofa a shekarar 1982 zuwa 1985. Daga nan ne ya rubuta jarabawar shiga Kwalejin Kimiyya da Fasaha, ya sami shiga Government Technical College Kano a shekarar 1985 zuwa 1988, inda ya kamala da samun Takardar Shaida ta Kwarewa a Fannin Ilmin Gyaran Lantarki (Electrician).

    Bayan kammala wannan karatu ne ya sami aiki cikin ikon Allah a Hukumar Kwastam Ta Kasa a shekarar 1991, a matsayin Mataimakin Kwastam mai matsayi na III. Daga nan ya tafi Makarantar Horon Aikin Kwastam dake Kano, a inda suka sami Horo na wata 6.

    Bayan kammala wannan aikin Horo ne aka tura shi Jihar Katsina da aiki. Bayan ya shafe tsawon shekara 3 a Jihar Katsina ne sai ya sami canjin wurin aiki, a inda aka dawo da shi Jihar Kano a shekarar 1996, yayi aiki ne a Malam Aminu Kano International Airport.

    Yanayin aiki ya sa an sake canza masa wurin aiki a shekarar 1999, inda aka tura shi aikin zuwa Jihar Port Harcourt. Bayan ya shafe shekara 3 a can, sai aka sake tura shi Jihar Enugu a shekara ta 2002.

    Ya yi aiki na tsawon shekara 2 a Enugu, kafin daga bisani aka mayar da shi babbar Shalkwatarsu ta Kasa da ke Abuja a shekarar 2004. Ya shafe shekara 4 a Shalkwata, kafin daga nan aka sake tura Jihar Lagos, a inda ya yi aiki dangaren Lagos, Tincon to Kano /Jigawa Area Command.

    A shekara ta 2002 bayan ya koma Abuja, sai ya yanke shawarar komawa Makaranta, a inda ya sami amincewar Shugaban da yake aiki a karkashinsa, kasancewar a lokacin yana da takardar Shaidar Karatu da ya yi a fannin Electrician. A nan ne ya nemi shawara daga Malam Ibrahim Mohammed Gandu, ya ba shi shawarar komawa karatu a FCE, Kano, inda ya yi karatu a bangaren gudanarwa Certificate of Administration (CA).

    Ya sami Takardar Karatu a kangaren Gudanarwa, bai tsaya da neman ilimi ba, sai da ya sake komawa Kwalejin Fasaha ta Kano, inda ya sami Karama (ND) da Babbar Takarda Diploma Ta Kasa a fannin Kasuwanci da Tattalin Arziki (HND) a tsakanin shekarun 2006 zuwa 2009.

    Bayan kammala wannan karatu ne a shekarar 2009 ya yi Jarabawar neman Karin Matsayi, inda ya sami Karin girma zuwa Assistant Supretendant II (ASC II). Daga nan tafiya ta ci gaba, inda a shekarar 2013, ya sake zuwa Jarawa ta neman karin matsayi zuwa Assistant Supretendant I (ASCI).

    A cikin shekarar 2013 ne bayan ya sami karin girma likkafa ta sake dagawa, aka zabe shi zuwa Sashen Customs Inteligent Unit. Ya je Lagos kwas na wata 3. Bayan ya kamala kwas din ne aka tura Lagos Sashen SAPID. Dagan an ne aka sake dawo da shi Kano, a shekara ta 2017 cikin ikon Allah ya sake samun ci gaban matsayi zuwa matakin Deputy Supretendant (DSC).

    A matakin shekara ajiye aiki ne Allah ya sake daga shi zuwa mukamin Supretendant of Custom (SC), matsayin da Allah ya nufe shi da ajiye aiki a kai.

    Custom mutum ne na kwarai da nagarta da son cigaban al’umma a duk inda ya sami kansa, Allah ya albarkaceshi da dukiya irin wadda Allah yake so, domin gwanine wajen taimakawa al’umma da wannan dukiyar tasa.

    Babban abin alfahari da shi wannan bawan Allah din shine, wallahi bai dauki kansa a kamai ba, ko wani mai kuɗi, yana da ladabi da biyayya ga kaskantar da kai daga na sama da shi har zuwa na kasa da shi.

    Alhamdulillah, Jaridar Alfijir Labarai na taya Alh Mukhtar Aliyu Custom murnar kammala aiki lafiya da fatan alheri a rayuwa bayan ritaya.

  • Bichi Teachers College Aji na 1980 Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai da Taimakon Juna

    Bichi Teachers College Aji na 1980 Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai da Taimakon Juna

    Kungiyar tsaffin dalibai ta Bichi Teachers College, aji na 1980, ta yi kira ga dukkan kungiyoyin ɗalibai da su ƙara maida hankali wajen tallafa wa junan su, musamman mambobin da ke cikin halin ƙaƙƙarfan rayuwa, domin ƙarfafa zumunci, haɗin kai da kuma bunƙasa jin daɗin al’umma baki ɗaya.

    Shugaban ƙungiyar, Alhaji Danlami Muhammad Fagge, ne ya bayyana wannan kira yayin taron sadar da zumunci da ƙungiyar ta gudanar a yau Lahadi.

    Ya bayyana cewa tallafawa juna na daga cikin muhimman manufofin ƙungiyar tsaffin dalibai, inda ya ce rashin kulawa da halin da wasu mambobi ke ciki kan iya kawo cikas ga zaman lafiya da ci gaban ƙungiya.

    Alhaji Danlami ya jaddada cewa haɗin kai da taimakon juna su ne ginshiƙan da suka sa tsofaffin ɗalibai ke ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki ɗaya tun bayan kammala karatu.

    Ya ce ƙungiyoyin tsaffin dalibai ba wai don haɗuwa kawai ake kafawa ba, har ila yau don tallafawa juna a lokutan ƙalubale kamar rashin aikin yi, matsalolin lafiya da kuma wasu buƙatun rayuwa.

    Ya kuma yi kira ga mambobin ƙungiyar da su ƙara himma wajen bayar da gudummawa, domin kafa asusun tallafi na musamman da za a rika amfani da shi wajen taimaka wa marasa ƙarfi, gami da tallafawa harkokin ilimi da na zamantakewa a cikin al’umma.

    A yayin taron, wasu daga cikin mambobin ƙungiyar sun bayyana ra’ayoyinsu, inda suka yabawa shugabannin ƙungiyar bisa ƙoƙarin da suke yi na ƙarfafa zumunci da haɗin kai.

    Wasu mahalarta taron sun bayar da shawarwari kan hanyoyin bunƙasa ayyukan ƙungiyar, musamman wajen amfani da ilimi da ƙwarewar mambobi don tallafa wa matasa da ɗalibai masu tasowa.

    Taron sadar da zumuncin ya samu halartar manyan tsaffin dalibai daga sassa daban-daban na ƙasar, inda aka yi addu’o’i na neman zaman lafiya da albarka, tare da ɗaukar wasu muhimman shawarwari da za su taimaka wajen ƙarfafa ayyukan ƙungiyar a nan gaba.

  • Rashin Kuɗi ne ya hana Hukumar Bayar da Ruwan sha ta Kano Mayar da Ma’aikatan Wucin-Gadi Din-Din

    Rashin Kuɗi ne ya hana Hukumar Bayar da Ruwan sha ta Kano Mayar da Ma’aikatan Wucin-Gadi Din-Din

    Hukumar bayar da ruwan sha ta jihar Kano ta ce matsalar rashin kuɗi a wannan shekara ta hana ta aiwatar da shirin mayar da ma’aikatan wucin-gadi zuwa na din-din.

    Shugaban hukumar, Garba Ahmad Bichi, ne ya bayyana haka bayan kammala kare kasafin kuɗin hukumar a gaban kwamitin ruwa na majalisar dokokin jihar Kano.

    Ya ce duk da adadin kuɗin da aka ware wa hukumar, akwai manyan kalubale da ke hana gudanar da ayyuka yadda ya kamata, musamman ma a ɓangaren kula da matatun ruwa da samar da sabbin wasu.

    Bichi ya bayyana cewa hukumar na ƙoƙarin inganta wadatar ruwan sha ga al’umma, amma har yanzu ba ta kai ga samar da adadin da ya dace ba saboda ƙarancin kuɗaɗen gudanarwa.

    Shugaban ya kara da cewa a sabon kasafin da aka gabatar, hukumar ta shirya aiwatar da gyare-gyare a matatun ruwa tare da sabunta wasu muhimman sassa domin rage matsalolin da ake fuskanta wajen samar da ruwa a Kano.

  • Gwamnan kano Ya Umurci kwamishinan Shari’a AG Maude da Ya Binciki Zargin Hari da Aka Yi wa Rabi Hamza Danladi Nasidi

    Gwamnan kano Ya Umurci kwamishinan Shari’a AG Maude da Ya Binciki Zargin Hari da Aka Yi wa Rabi Hamza Danladi Nasidi

    Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya nuna matuƙar damuwa kan mummunan harin da Rabi Hamza Danladi Nasidi ta ce an kai mata, wanda ake zargin wani Kabiru Aminu ya aikata a gidanta. Rahotanni sun nuna cewa an ji mata mummunan rauni da wuka a bakinta, lamarin da ya hana ta cin abinci tare da jefa lafiyarta cikin halin ƙunci.

    Duk da cewa an fara tura wanda ake zargi gidan yari ta kotun Majistare mai lamba 36 har zuwa ranar 20 ga Janairu, 2026, daga baya wanda abin ya shafa ta ga alamar an sake shi, abin da ya haifar da damuwa a tsakanin jama’a. A cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, Rabi Hamza Danladi Nasidi ta roƙi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya sa baki domin tabbatar da adalci.

    Da zarar Gwamna Abba ya samu labarin faruwar lamarin, ya nuna damuwar sa kan taɓarɓaren yadda aka gudanar da shari’ar, tare da hanzarta umartar Babban Lauyan Jiha kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, da ya gudanar da cikakken bincike tare da ɗaukar duk matakan shari’a da suka dace.

    Babban Lauyan Jiha ya tabbatar wa Gwamnan cewa za a gudanar da cikakken bincike, kuma duk wanda aka samu da hannu a lamarin za a ɗauki mataki a kan sa bisa tanadin doka.

    Gwamnati ta jaddada kudurinta na kare ‘yancin jama’a, tabbatar da walwala da jin daɗin al’umma, da kuma tabbatar da adalci ba tare da tsoro ko son zuciya ba.

  • An Kaddamar da Sabuwar Hukumar Hisbah Gandujiyya a Kano

    An Kaddamar da Sabuwar Hukumar Hisbah Gandujiyya a Kano

    An kaddamar da fom ɗin neman shiga kungiyar Hisbah Gandujiyya a ranar Asabar 6 ga Disamba 2025 a Kano, ƙarƙashin jagorancin jigon jam’iyyar APC, Hon. Baffa Babba Dan Agundi.

    Taron ya samu halartar tsohon kwamandan Hisbah na jihar Kano, Sheikh Harun Ibn Sina, wanda ya jaddada muhimmancin samar da tsari mai inganci wajen kare tarbiyya da kyawawan ɗabi’u cikin al’umma.

    Majiyar Arewa Update ta rawaito cewa ƙaddamarwar ta kasance mataki na farko na shirye-shiryen da kungiyar Hisbah Gandujiyya ke yi domin farfaɗo da ayyukan da ta bayyana cewa sun tsaya cik bayan korar daruruwan ma’aikata a baya.

    Kungiyar ta sanar da cewa tana kan gyara manyan tsare-tsarenta da za su taimaka wajen tallafawa al’umma, musamman matasa da wadanda ke cikin halin rashin aiki a Kano.

    A cewar kungiyar, kusan mutane dubu goma sha biyu da ta ce an kora daga Hisbah ta gwamnati a baya ne za su amfana da sabon tsarin da suka tanada.

    Haka kuma an bayyana cewa kwamandojin sabuwar Hisbah daga kananan hukumomi 44 na jihar da wasu daga cikin jami’ansu ne suka halarci taron na ƙaddamarwar.

    Hon. Dan Agundi ya bayyana cewa sabon tsarin zai mayar da hankali kan aiwatar da doka da oda cikin lumana, tare da nisantar da kungiyoyin matasa daga aikata miyagun laifuka.

    Kungiyar ta Hisbah Gandujiyya ta sha alwashin yin aiki cikin gaskiya da adalci, tare da tabbatar da cewa sabbin matakan da za su aiwatar za su inganta zaman lafiya da tsaro a fadin jihar Kano.