Rahotanni daga DAILY NIGERIAN sun tabbatar da cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zai sauya sheƙa daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a hukumance ranar Litinin mai zuwa.
Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa gwamnan ya riga ya isa Abuja domin kammala shirye-shiryen ficewarsa daga NNPP.
Rahoton ya ce Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, tare da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Yitwalda Nentawe, ne za su karɓi gwamnan a birnin tarayya.
Haka kuma, an tabbatar da cewa jagoran APC a Kano, Abdullahi Ganduje, an kira shi da gaggawa daga tafiyar da yake yi a Dubai.
A gefe guda kuma, shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya rage zamansa a Umrah domin shirya ba gwamnan katin zama ɗan APC a Diso Ward, Karamar Hukumar Gwale a cikin makon nan.
Idan hakan ta tabbata, Abba Kabir Yusuf zai zama gwamnan NNPP na ƙarshe da ya bar jam’iyyar, lamarin da ke ƙara ɗaga kura a fagen siyasar Kano da Arewa baki ɗaya.

Leave a Reply