Hukumar Shari’a ta jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ta gudanar da shan ruwa tare da waɗanda suka karɓi addinin Musulunci a Kano.
Kwamishina na biyu a hukumar Shari’a ta jihar Kano, Sheikh Ali Ɗan Abba, ne ya jagoranci taron shan ruwan a harabar hukumar.
Waɗanda suka musulunta, da manyan baƙi, haɗi da daraktoci da sauran shugabannin hukumar shari’ar da dama ne suka samu damar halartar taron shan ruwan.
Da yake jawabi a yayin taron, Sheikh Ali Ɗan Abba, ya ce hukumar shari’ar, ta gudanar da shan ruwan tare da waɗanda suka musuluntar ne bisa sahalewar Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, inda ake shirya wa duk cikin watan azumin Ramadan, domin sanya musu farin ciki, a kuma yi addu’a ta musamman.
A jawabinsa Wakilin Shugaban Kungiyar Taimakon Musulunci ta World Association of Muslim Youth WAMY, Malam Sunusi Ibrahim, ya bayyana cewar wannan tsari da ake yi abun a yaba ne tare da jinjinawa.
A yayin taron shan ruwan, an kuma yi wa jihar Kano, da gwamnatin jihar ƙarkashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, addu’a, tare da ƙara samun zaman lafiya, da ci gaba mai ɗorewa a jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya.

Leave a Reply