Khalid Yusuf Idris Ya Ajiye Aiki a Rahma TV, Ya Kaddamar da Sabuwar Kafar Zamani “KANO LIVE 24″

Shugaban Sashin Rahma TV da kuma Sashin Kafafen Sada Zumunta na tashar, Khalid Yusuf Idris, ya ajiye aikinsa a hukumance a tashar Rahma TV, domin mayar da hankali kan sabuwar kafar zamani da ya assasa mai suna KANO LIVE 24.
Wani makusanci ga Khalid Yusuf Idris ne ya tabbatarwa Newshub24 wannan mataki, inda ya bayyana cewa shawarar ta biyo bayan dogon nazari, shawarwari da kuma burin samar da kafar yaɗa labarai ta zamani wadda za ta mayar da hankali kan sahihanci, sauri da kuma buƙatun al’umma a wannan zamani na fasaha.
Majiyoyinmu sun nuna cewa Khalid Yusuf Idris ya shafe shekaru yana taka muhimmiyar rawa a Rahma TV, musamman wajen jagorantar sashen kafafen sada zumunta da kuma bunƙasa ayyukan tashar a duniyar zamani.
A tsawon lokacin da ya yi a tashar, ya taimaka wajen inganta tsarin watsa labarai, haɓaka hulɗa da masu kallo da kuma isar da labarai cikin sauri da nagarta.
A cewar majiyoyi, tafiyarsa daga Rahma TV ta gudana ne cikin mutunta juna da fahimta, inda bangarorin biyu suka yaba da irin gudunmawar da ya bayar a lokacin aikinsa, tare da yi masa fatan alheri a sabon babi na rayuwarsa ta sana’a.
Sabuwar kafar KANO LIVE 24 na da burin zama sahihiyar majiyar labarai ta zamani, wadda za ta rika watsa labarai kai tsaye, rahotanni na musamman, shirye-shiryen tattaunawa, bayanai kan harkokin siyasa, zamantakewa, tsaro, tattalin arziki da kuma abubuwan da suka shafi rayuwar al’umma.
Baya ga haka, kafar za ta yi amfani da hanyoyin zamani na kafafen sada zumunta domin kai wa jama’a labarai cikin gaggawa, tare da ba su damar yin mu’amala kai tsaye da shirye-shiryen da ake gabatarwa.
Masana harkokin yaɗa labarai na ganin cewa ƙaddamar da KANO LIVE 24 zai ƙara faɗaɗa fagen yaɗa labarai a Jihar Kano da Arewa baki ɗaya, tare da samar da sabuwar dama ga matasa masu sha’awar aikin jarida da kafafen zamani.
Ana sa ran kafar za ta fara aiki a hukumance nan ba da jimawa ba, inda za ta kawo sabbin tsare-tsare da dabaru domin biyan bukatun masu sauraro da masu kallo a wannan zamani.




