Hukumar Shari’ar Kano Ta Shawarci Iyaye Su Rinka Sanya ’Ya’yansu a Gaba Yayin Zuwa Sallar Tuhajjud

IMG 20260310 WA0004

Hukumar Shari’a ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ta buƙaci iyaye da su rinƙa sanya ’ya’yansu a gaba, musamman ’yan mata, yayin da suke zuwa sallar dare ta Tuhajjud a wannan wata na Ramadan, domin kare su daga haɗuwa da wasu bata-gari da ka iya ɓata musu tarbiyya.

Kwamishina na biyu na Hukumar Shari’ar Jihar Kano, Sheikh Ali Ɗan Abba, ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan da ya jagoranci saɓunta wasu kwamitocin hukumar guda biyu. Kwamitocin sun haɗa da Kwamitin Sulhu da kuma Kwamitin Tantance Limamai.

An gudanar da taron saɓunta kwamitocin ne a ɗakin taro na hukumar da ke Kano.

Sheikh Ali Ɗan Abba ya bayyana cewa sanya ’yan mata a gaba tare da iyayensu yayin zuwa masallaci domin halartar sallar Tuhajjud zai taimaka wajen kare su daga gurɓacewar tarbiyya.

Ya kuma ƙara da cewa an saɓunta kwamitocin ne biyo bayan rushe tsoffin kwamitoci guda huɗu da suke a baya, inda aka haɗa su zuwa kwamitoci biyu domin ƙara inganta ayyukan addini da kuma ci gaban al’umma a sassan jihar.

A yayin ƙaddamar da sabbin kwamitocin, Kwamishina na biyu Sheikh Ali Ɗan Abba ya kasance tare da Kwamishina na ɗaya, Gwani Hadi Ɗahiru Yakasai, da wasu daga cikin mambobin hukumar gudanarwa, da kuma mambobin sabbin kwamitocin.

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *