Gwamnatin kano ta ce ba za tayi watsi da matasan da suka tuba ba

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusif ta bayyana cewa ba za ta yi watsi da matasan da suka tuba daga harkar fadace fadacen daba ba, domin kuwa suna da baiwar da suke da ita wacce za ta amfanar da al’umma muddin aka basu kulawar da ta dace.
Kwamishinan Yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron da aka shirya domin karɓar wasu daga cikin matasan da suka yanke shawarar barin harkar daba.
Kwamishinan ya bayyana cewa zuwa yanzu an tantance matasa sama da dubu 1 da 600 da aka saka cikin shirin Safe Corridor, kuma nan gaba kadan za’a ci gaba da tantance wasu matasa 2,100 domin su ma su shiga cikin shirin.
Haka kuma ya ce bayan kammala wannan mataki za a mika su gaban gwamna domin karɓar tallafin da zai basu na dogaro da kansu.
Waiya ya tabbatar da cewa gwamnatin kano za ta ci gaba da tallafawa matasan da suka nuna dabi’u masu kyau wajan samun ingantacciyar rayuwa.
Da yake nasa jawabin a madadin maimartaba sarkin Kano Dan Amar din Kano Alhaji Aliyu Harazimi ya bukaci Matasan da su dage wajen komawa ga Allah, domin hakan yana kawar da mutane daga aikata abubun da basu dace ba
wannan shine karo na uku da kwamishin na yada labarai da harkokin cikin gida na kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya jagoranci zaman tattaunawa da kwamitin zaman lafiya na safe Corridor domin cigaba da tattance su da kuma samar da hanyoyin cika musu alkawarin da gwamnatin kano ta dauka a kansu.




