Kungiyar Tuntuba ta Arewa ta Shirya Gasar Sada Zumunci ta Jihohi Bakwai a Kano

Kungiyar Tuntuba ta Arewa ta shirya wasan sada zumunci na ƙwallon ƙafa tsakanin jihohi bakwai na Arewacin ƙasar nan, a wani ɓangare na bikin cika shekaru 25 da kafuwar ƙungiyar.
Newshub24hausa ta rawaito Shugaban shirye-shiryen gasar, Dakta Abubakar Sadiq Sa’adu Fakai, ya bayyana cewa wasan zai gudana na tsawon kwanaki uku a Jihar Kano, tare da nufin ƙarfafa zumunci da haɗin kai tsakanin jihohin Arewa.
Ya ce gasar ta haɗa jihohi guda bakwai da suka haɗa da Kano, Katsina, Jigawa, Kaduna, Sokoto, Zamfara da Kebbi, inda kowace jiha za ta fafata domin lashe kofin sada zumunci.

A nasa jawabin, ɗaya daga cikin mambobin kwamitin shirya wasannin, Sharif, ya bayyana cewa an tanadi kyaututtuka da dama ga ƙungiyar da ta yi fice a gasar.
Haka kuma, wani mamba a kwamitin, Abdulhamid Abdullahi Dan Ketko, ya ce gasar za ta zama wata hanya ta gano sababbin hazikan matasa da za su iya wakiltar ƙasarsu a manyan matakai na ƙasa da ƙasa.

Ya ƙara da cewa kungiyar ta ɗauki wannan mataki ne domin tallafa wa harkokin wasanni da kuma inganta haɗin kan al’ummar Arewa.
Masu shirya gasar sun kuma bayyana cewa za a kaddamar da gasar a filin wasa na Sani Abacha dake cikin birnin Kano, inda za a samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na ƙasar.
An tsara gudanar da wasan daga Laraba zuwa juma’a, tare da fatan cewa wannan aiki zai ƙarfafa zumunci da haɗin kai tsakanin al’ummomin Arewa baki ɗaya.