labarai

Gwamnatin Tarayya ta ɗau alwashin ceto ɗalibai mata da aka sace a Kebbi

Gwamnatin Tarayya ta bayyana damuwa matuƙa kan sace ɗalibai mata na Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata da ke Maga, a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa.

A wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya fitar, gwamnati ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa kare rayukan ’yan ƙasa, musamman na ɗalibai, na daga cikin manyan nauyikan da gwamnatin tarayya ke ɗauka a matsayin wajibi.

Gwamnatin ta yi Allah wadai da harin da maharan suka kai, wanda ya yi sanadiyyar kashe wasu jami’an makarantar tare da yin garkuwa da ɗaliban.

Ministan ya ce an bai wa hukumomin tsaro da leƙen asiri umarni kai tsaye da su binciko inda ’yan makarantar suke, su ceto su lafiya, sannan su tabbatar da cewa masu laifin sun fuskanci hukunci. Ya ce gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an kammala wannan aiki.

Ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya na ƙara ƙaimi wajen inganta tsaro a cikin gida, ciki har da sake fasalin rundunonin soja, ’yan sanda, da na leƙen asiri domin samar da martani cikin sauri da inganci ga duk wata barazana.

Sanarwar ta kuma nuna cewa Najeriya na ƙara haɗin gwiwa da ƙasashen yankin ta hannun ECOWAS, Ƙungiyar Tarayyar Afirka, da Rundunar haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa ta MNJTF, domin ƙarfafa tsaron iyakoki da karya ƙungiyoyin ta’addanci da masu garkuwa da mutane.

Ministan ya yi kira ga ’yan ƙasa da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da bai wa hukumomin tsaro goyon baya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button