Karota ta yi alƙawarin mika buƙatun ɗaliban Jami’ar Sule Lamido ga hukumomin da suka dace

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Jihar kano (KAROTA) tayi alkawarin mika bukatun daliban Jami’ar Sule Lamido dake Kafin Hausa, a Jihar Jigawa, ‘yan asalin Jihar Kano, domin magance musu matsalolin sufuri daga Kano zuwa Jihar Jigawa.
Shugaban hukumar KAROTA, Hon. Faisal Mahmud Kabir, ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi baƙuncin ƙungiyar daliban Jami’ar Sule Lamido dake Kafin Hausa, a makon da ya gabata.
Cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na Hukumar, Abubakar Ibrahim Sharada, ya fitar a yau Lahadi, 2 ga watan Nuwamba 2025.
shugaban hukumar ya kuma bukaci daliban da su kasance jakadu na gari, waɗanda Jihar Kano za ta yi alfahari da su a nan gaba.
Hon. Faisal ya ƙara da cewa, hukumar za ta tuntubi ma’aikatar Aiyuka domin samar musu da dakunan kwana ga daliban Jihar Kano sama da 4,000, domin rage musu kuɗin masauki, Da kuma tallafa musu wajen samun ilimi cikin sauƙi.
A nasa jawabin, shugaban ƙungiyar daliban Jami’ar Sule Lamido dake Kafin Hausa, Comrade Habibu Abdullahi Abubakar, ya bayyana cewa sun kai wannan ziyara ne domin miƙa buƙatun ƙungiyar, tare da ƙara ƙarfafa alaƙar haɗin gwiwa tsakanin daliban da hukumar KAROTA.
A ƙarshe, shugaban hukumar KAROTA, Hon. Faisal Mahmud Kabir, ya gode wa daliban bisa wannan ziyara da suka kawo masa, tare da bayar da tabbacin cewa hukumar za ta ci gaba da tallafa musu duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.




