DA ƊUMI ƊUMISA: Jami’an Tsaro Sun Kama Wanda Ake Zargi da Kashe Mata da ’Ya’yanta Guda Shida a Dorayi

Rahotanni da ke shigowa sun tabbatar da cewa jami’an tsaro sun kama wanda ake zargi da kashe wata mata tare da ’ya’yanta guda shida a unguwar Dorayi, da ke cikin birnin Kano.
Wani mazaunin yankin, da ya nemi a sakaya sunan sa, ya shaida mana cewa an kama wanda ake zargin ne da misalin ƙarfe 2 na dare, bayan samun bayanan sirri tare da haɗin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da mazauna unguwar.
A cewar rahotannin da aka samu, kamen ya biyo bayan bincike mai zurfi kan wannan mummunan lamari da ya girgiza al’ummar Dorayi tare da jefa al’ummar jihar Kano cikin alhini da kaduwa.
Mazauna yankin sun bayyana matuƙar jimami da tashin hankali bisa wannan lamari, inda suka yi kira ga hukumomi da su tabbatar da cikakken bincike mai zaman kansa, domin ganin an tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya shafa.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da cikakken bayani a hukumance ba, sai dai sun tabbatar da cewa wanda ake zargi yana hannunsu kuma ana ci gaba da bincike domin gano hakikanin gaskiyar abin da ya faru.
Za mu ci gaba da bibiyar wannan lamari tare da kawo muku ƙarin bayani da zarar an samu.




