labaraiTsaro

Gwamna Abba Ya yi Kira ga Jama’ar Kano Su ƙara Addu’a Kan Matsalar Tsaro

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kira ga mazauna jihar da su ƙara tsananta addu’o’i domin samun zaman lafiya da kariyar Allah, sakamakon ƙalubalen tsaro da ke tasowa a jihar, ciki har da ƙaruwa a hare-haren ‘yan bindiga.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a wani taron addu’a na musamman da gwamnatin jihar ta shirya, wanda aka gudanar a filin taro na Open Arena cikin fadar gwamnatin Kano.

Gwamna Yusuf ya bayyana addu’a a matsayin “makami mafi ƙarfi wajen yakar sharrin mugaye da duk wanda ke neman cutar da bil’adama,” inda ya nanata muhimmancin hadin-kai a addu’a domin kare jihar.

Ya roƙi malamai da shugabannin addini su ci gaba da jagorantar al’umma wajen yin addu’o’in neman zaman lafiya mai ɗorewa a Kano.

Gwamnan ya nuna damuwa kan hare-haren ‘yan bindiga da aka samu a wasu yankuna na jihar kwanakin baya, yana mai cewa lamarin baƙon abu ne, kuma na buƙatar rokon Ubangiji domin kawo sauki.

Ya bayyana cewa duk da cewa gwamnati na ƙoƙarin ƙarfafa matakan tsaro, addu’a dole ta taimaka wajen cike gibi tare da ƙarfafa waɗannan matakai.

A nasa jawabin, Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga jama’a da su ƙara jajircewa wajen yin addu’a domin zaman lafiya, cigaba da haɗin kan Kano.

Sarkin ya yaba wa gwamnatin jihar bisa tsara taron addu’ar, yana mai cewa babban abin bukata ne ganin halin da ake ciki na tsaro a wasu yankunan jihar.

Taron addu’ar na musamman ya kunshi karatun Alƙur’ani da addu’o’i na musamman da manyan malamai daga sassa daban-daban suka jagoranta.

Masu halarta sun roƙi rahamar Allah, kariya da shiriya domin kawo ƙarshen matsalolin tsaro tare da tabbatar da ci gaba a cikin Jihar Kano.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button