Rashin Kuɗi ne ya hana Hukumar Bayar da Ruwan sha ta Kano Mayar da Ma’aikatan Wucin-Gadi Din-Din

Hukumar bayar da ruwan sha ta jihar Kano ta ce matsalar rashin kuɗi a wannan shekara ta hana ta aiwatar da shirin mayar da ma’aikatan wucin-gadi zuwa na din-din.
Shugaban hukumar, Garba Ahmad Bichi, ne ya bayyana haka bayan kammala kare kasafin kuɗin hukumar a gaban kwamitin ruwa na majalisar dokokin jihar Kano.
Ya ce duk da adadin kuɗin da aka ware wa hukumar, akwai manyan kalubale da ke hana gudanar da ayyuka yadda ya kamata, musamman ma a ɓangaren kula da matatun ruwa da samar da sabbin wasu.
Bichi ya bayyana cewa hukumar na ƙoƙarin inganta wadatar ruwan sha ga al’umma, amma har yanzu ba ta kai ga samar da adadin da ya dace ba saboda ƙarancin kuɗaɗen gudanarwa.
Shugaban ya kara da cewa a sabon kasafin da aka gabatar, hukumar ta shirya aiwatar da gyare-gyare a matatun ruwa tare da sabunta wasu muhimman sassa domin rage matsalolin da ake fuskanta wajen samar da ruwa a Kano.




