Lafiyalabarai

Gwamnatin kano Ta Yi Kira Ga Jama’a Su Rika Duba Lafiyarsu Don Rigakafin Ciwon Siga

Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci al’umma da su rika zuwa cibiyoyin lafiya akai-akai domin yin gwaje-gwajen lafiya don kare kansu daga kamuwa da cutar sikari, wadda mutane da dama ke fama da ita ba tare da sun sani ba.

Yayin bikin Ranar Masu Fama da Cutar Siga ta Duniya da aka gudanar a yau, wanda aka yi masa taken “Ciwon Siga a Kowane Mataki na Rayuwa,” Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya jaddada muhimmancin gano cutar da wuri da yin gwajin lafiya lokaci-lokaci.

A cewar kwamishinan, yawan mutanen da ke kamuwa da ciwon siga na ƙaruwa, kuma hakan na faruwa ne sakamakon rashin gano matsalar da wuri da kuma rashin zuwa yin gwaji. Ya ce gwamnati na ci gaba da inganta cibiyoyin kiwon lafiya domin sauƙaƙa wa jama’a samun damar yin gwaje-gwaje da kuma samun kulawa yadda ya kamata.

Dakta Abubakar ya bayyana cewa ciwon siga na daga cikin manyan matsalolin lafiya da ke addabar jama’a, musamman idan ba a gano shi tun farko ba, domin hakan na jawo matsaloli da raɗaɗi ga masu fama da shi.

Kwamishinan ya yi kira ga iyaye da matasa da su rungumi cin abinci mai kyau, tare da yin motsa jiki akai-akai, yana mai cewa waɗannan matakai na taka muhimmiyar rawa wajen rage haɗarin kamuwa da ciwon siga.

Haka kuma, ya shawarci masu fama da cutar da su rika bin dukkan shawarwarin likitoci domin kula da lafiyarsu da kuma sarrafa cutar yadda ya kamata.

Dakta Abubakar ya kara da cewa gwamnatin jihar Kano za ta ci gaba da wayar da kan jama’a game da hanyoyin kariya da kuma kula da masu fama da ciwon siga a fadin jihar.

A ƙarshe, ya yi kira ga shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki da su mara wa gwamnati baya wajen fadakar da jama’a kan muhimmancin kula da lafiya da yin gwaje-gwaje lokaci-lokaci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button