labarai

Iyaye Sun Koka Kan Kuɗin Yaye Dalibai ₦750,000 a Jami’ar Maryam Abacha Kano

Kungiyar iyayen dalibai masu karatu a Jami’ar Maryam Abacha da ke Kano sun nemi Hukumar Karɓar Korafe-korafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano da ta sanya baki kan ƙorafin da suka gabatar game da kuɗin shirye-shiryen bikin yaye dalibai da jami’ar ta ƙayyade, wanda ya kai naira dubu 750.

Iyayen sun bayyana cewa adadin kuɗin ya yi tsauri matuƙa fiye da yadda ya dace, lamarin da ke haifar da nauyi mai yawa ga iyaye da masu kula da dalibai.

Da yake magana da manema labarai, ɗaya daga cikin iyayen daliban, Alhaji Yusuf Muhammad, ya ce sun nemi agajin hukumar ne saboda ganin cewa kuɗin da aka saka bai yi daidai da yanayin tattalin arzikin da ake ciki ba. Ya ce abin ya jefa iyalai da dama cikin damuwa, saboda barazanar da jami’ar ta yi cewa duk dalibin da bai biya kuɗin ba ba za a bashi takardar kammala karatu ba.

Haka kuma, Hajiya Fatima Itama, ɗaya daga cikin iyayen da yaransu za su kammala karatu, ta ce tsadar kuɗin ta sanya iyaye da dama cikin tashin hankali, inda wasu ke ganin hakan na iya hana ’ya’yansu samun takardar kammala karatu duk da wahalar da suka sha wajen biyan kudaden makaranta a tsawon shekaru.

A nasa jawabin, shugaban Hukumar Karɓar Korafe-korafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Kano, Sa’idu Yahaya, ya tabbatar da cewa sun karɓi ƙorafin iyayen daliban, kuma hukumar za ta gudanar da bincike mai zurfi domin samar da adalci a tsakanin bangarorin da abin ya shafa.

Ya ce hukumar za ta tattauna da shugabancin jami’ar domin jin ta bakinsu, tare da bincikar duk bayanan da suka shafi kuɗin da ake ƙorafi a kansa, domin tabbatar da cewa an bi ka’ida kuma ba a ɗora wa iyaye abin da ya wuce ƙarfin su ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button