labarai

Majalisar Dokokin Kano Za Ta Kafa Doka Kan Koyar da Kimiyya da Fasaha da Harshen Uwa

Majalisar dokokin jihar Kano ta shirya samar da doka da za ta bai wa malamai damar koyar da darussan kimiyya da fasaha da harshen uwa a makarantun jihar, domin kara inganta fahimtar ɗalibai da kuma tabbatar da cewa tsarin ilimi ya dace da yanayin su na gida.

Dan majalisar dokoki mai wakiltar Takai, Hon Dakta Musa Ali Kachako, ne ya gabatar da wannan kudiri a zaman majalisar, inda ya bukaci a kafa doka bisa tanadin Manufar Harshen Kasa ta shekarar 2022, wacce ta tanadi koyar da darussa da harshen uwa a matakin Firamare da na ƙaramin Sakandare.

Newshub24 Hausa ta rawaito Dokta Kachako ya bayyana cewa, koyar da kimiyya da fasaha da harshen gida zai ba dalibai damar fahimtar darussa cikin sauƙi, tare da haɓaka sha’awarsu wajen nazari da gwaje-gwaje. Ya ce hakan zai taimaka wajen samar da ƙarni na matasa masu kwarewa da ƙwazo a fannoni na kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire, wanda zai taimaka wajen ci gaban jihar da ƙasa baki ɗaya.

Ya kara da cewa, tsarin koyarwa da harshen uwa yana da muhimmanci wajen kare harsunan gida daga bacewa, tare da tabbatar da cewa al’adun gargajiya suna ci gaba da wanzuwa a tsakanin matasa. A cewarsa, harshen uwa shi ne ginshikin ilimi, domin shi ɗalibai ke fara fahimta tun suna ƙanana, kuma hakan na haifar da gagarumin tasiri ga nasu cigaban tunani.

Wasu ‘yan majalisar da suka tofa albarkacin bakinsu, sun bayyana goyon bayansu ga wannan kudiri, inda suka ce lokaci ya yi da za a canza tsarin koyarwa daga dogaro da harshen Turanci zuwa amfani da harsunan gida kamar Hausa, Fulfulde, da Kanuri domin ya zama tsarin ilimi mai tushe da amfani ga ɗalibai.

Majalisar ta kuma jaddada bukatar aiwatar da wannan kudiri cikin gaggawa, tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Ilimi da sauran hukumomin da abin ya shafa, domin tabbatar da ingantaccen shiri na koyarwa, fassarar littattafai da horas da malamai da zasu iya koyar da kimiyya da fasaha da harshen uwa.

A ƙarshe, majalisar ta bayyana cewa wannan doka idan aka kafa ta, za ta zama sabuwar kafa ta ci gaban ilimi a jihar Kano, wacce za ta taimaka wajen samar da ingantattun ɗalibai da ke fahimtar darussa cikin sauƙi tare da kare harshen uwa da al’adun yankin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button