Blog

  • Rashin Kuɗi ne ya hana Hukumar Bayar da Ruwan sha ta Kano Mayar da Ma’aikatan Wucin-Gadi Din-Din

    Rashin Kuɗi ne ya hana Hukumar Bayar da Ruwan sha ta Kano Mayar da Ma’aikatan Wucin-Gadi Din-Din

    Hukumar bayar da ruwan sha ta jihar Kano ta ce matsalar rashin kuɗi a wannan shekara ta hana ta aiwatar da shirin mayar da ma’aikatan wucin-gadi zuwa na din-din.

    Shugaban hukumar, Garba Ahmad Bichi, ne ya bayyana haka bayan kammala kare kasafin kuɗin hukumar a gaban kwamitin ruwa na majalisar dokokin jihar Kano.

    Ya ce duk da adadin kuɗin da aka ware wa hukumar, akwai manyan kalubale da ke hana gudanar da ayyuka yadda ya kamata, musamman ma a ɓangaren kula da matatun ruwa da samar da sabbin wasu.

    Bichi ya bayyana cewa hukumar na ƙoƙarin inganta wadatar ruwan sha ga al’umma, amma har yanzu ba ta kai ga samar da adadin da ya dace ba saboda ƙarancin kuɗaɗen gudanarwa.

    Shugaban ya kara da cewa a sabon kasafin da aka gabatar, hukumar ta shirya aiwatar da gyare-gyare a matatun ruwa tare da sabunta wasu muhimman sassa domin rage matsalolin da ake fuskanta wajen samar da ruwa a Kano.

  • Gwamnan kano Ya Umurci kwamishinan Shari’a AG Maude da Ya Binciki Zargin Hari da Aka Yi wa Rabi Hamza Danladi Nasidi

    Gwamnan kano Ya Umurci kwamishinan Shari’a AG Maude da Ya Binciki Zargin Hari da Aka Yi wa Rabi Hamza Danladi Nasidi

    Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya nuna matuƙar damuwa kan mummunan harin da Rabi Hamza Danladi Nasidi ta ce an kai mata, wanda ake zargin wani Kabiru Aminu ya aikata a gidanta. Rahotanni sun nuna cewa an ji mata mummunan rauni da wuka a bakinta, lamarin da ya hana ta cin abinci tare da jefa lafiyarta cikin halin ƙunci.

    Duk da cewa an fara tura wanda ake zargi gidan yari ta kotun Majistare mai lamba 36 har zuwa ranar 20 ga Janairu, 2026, daga baya wanda abin ya shafa ta ga alamar an sake shi, abin da ya haifar da damuwa a tsakanin jama’a. A cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, Rabi Hamza Danladi Nasidi ta roƙi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya sa baki domin tabbatar da adalci.

    Da zarar Gwamna Abba ya samu labarin faruwar lamarin, ya nuna damuwar sa kan taɓarɓaren yadda aka gudanar da shari’ar, tare da hanzarta umartar Babban Lauyan Jiha kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, da ya gudanar da cikakken bincike tare da ɗaukar duk matakan shari’a da suka dace.

    Babban Lauyan Jiha ya tabbatar wa Gwamnan cewa za a gudanar da cikakken bincike, kuma duk wanda aka samu da hannu a lamarin za a ɗauki mataki a kan sa bisa tanadin doka.

    Gwamnati ta jaddada kudurinta na kare ‘yancin jama’a, tabbatar da walwala da jin daɗin al’umma, da kuma tabbatar da adalci ba tare da tsoro ko son zuciya ba.

  • An Kaddamar da Sabuwar Hukumar Hisbah Gandujiyya a Kano

    An Kaddamar da Sabuwar Hukumar Hisbah Gandujiyya a Kano

    An kaddamar da fom ɗin neman shiga kungiyar Hisbah Gandujiyya a ranar Asabar 6 ga Disamba 2025 a Kano, ƙarƙashin jagorancin jigon jam’iyyar APC, Hon. Baffa Babba Dan Agundi.

    Taron ya samu halartar tsohon kwamandan Hisbah na jihar Kano, Sheikh Harun Ibn Sina, wanda ya jaddada muhimmancin samar da tsari mai inganci wajen kare tarbiyya da kyawawan ɗabi’u cikin al’umma.

    Majiyar Arewa Update ta rawaito cewa ƙaddamarwar ta kasance mataki na farko na shirye-shiryen da kungiyar Hisbah Gandujiyya ke yi domin farfaɗo da ayyukan da ta bayyana cewa sun tsaya cik bayan korar daruruwan ma’aikata a baya.

    Kungiyar ta sanar da cewa tana kan gyara manyan tsare-tsarenta da za su taimaka wajen tallafawa al’umma, musamman matasa da wadanda ke cikin halin rashin aiki a Kano.

    A cewar kungiyar, kusan mutane dubu goma sha biyu da ta ce an kora daga Hisbah ta gwamnati a baya ne za su amfana da sabon tsarin da suka tanada.

    Haka kuma an bayyana cewa kwamandojin sabuwar Hisbah daga kananan hukumomi 44 na jihar da wasu daga cikin jami’ansu ne suka halarci taron na ƙaddamarwar.

    Hon. Dan Agundi ya bayyana cewa sabon tsarin zai mayar da hankali kan aiwatar da doka da oda cikin lumana, tare da nisantar da kungiyoyin matasa daga aikata miyagun laifuka.

    Kungiyar ta Hisbah Gandujiyya ta sha alwashin yin aiki cikin gaskiya da adalci, tare da tabbatar da cewa sabbin matakan da za su aiwatar za su inganta zaman lafiya da tsaro a fadin jihar Kano.

  • Gwamna Abba Ya yi Gargadi Kan Siyasantar da Batun Tsaro,Ya Nemi Hadin Kan Jama’a Wajen Yakar ’Yan Bindiga

    Gwamna Abba Ya yi Gargadi Kan Siyasantar da Batun Tsaro,Ya Nemi Hadin Kan Jama’a Wajen Yakar ’Yan Bindiga

    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gargadi ‘yan Najeriya da su guji siyasantar da batutuwan tsaro, yana mai jaddada cewa barazanar da ‘yan bindiga ke kawo wa ta shafi kowa ba tare da la’akari da jam’iyya ko ra’ayin siyasa ba.

    Gwamnan ya yi wannan gargadin ne a ranar Asabar yayin wani taron addu’a na musamman tare da karatun Alƙur’ani da aka gudanar a fadar gwamnatin Kano, inda mahardatan Alƙur’ani 4,444 suka hallara domin neman taimakon Allah kan hare-haren ’yan bindiga da suka faru kwanan nan.

    Taron ya samu halartar Sarkin Kano na 16 daga Fulani, Muhammadu Sanusi II, tare da manyan jami’an gwamnati da shugabannin addini.

    Gwamna Yusuf ya jaddada cewa matsalar tsaro “ba ta san siyasa ko jam’iyya ba,” yana mai cewa wajibi ne daukar mataki tare-tare domin yakar miyagun laifuka.

    “Muna son ganin kowa ya hada hannu wurin yakar wannan annoba domin a kubutar da Kano,” inji shi.

    Ya ce gwamnatinsa ta samar wa hukumomin tsaro kayayyakin aiki da suka dace domin kara inganta ayyukansu, kana yana nan yana tattaunawa da su akai-akai domin magance bukatun da ke tasowa.

    Gwamnan ya roki jama’ar Kano da su kwantar da hankalinsu, yana tabbatar musu cewa gwamnati da jami’an tsaro na aiki ba dare ba rana domin kare jihar Kano da kewaye.

    Yusuf ya bayyana cewa wannan taron addu’a ba wai kudin da aka kashe ba ne kawai, har ma wata zuba jari ce ta ruhi da duk mai kishin jihar ya kamata ya tallafa mata.

    Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tare da masu sarauta da malamai don dawo da zaman lafiya mai dorewa a jihar.

    A nasa jawabin, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yaba wa gwamnatinsu kan wannan yunkuri, yana mai kiran shi babban mataki ne a lokaci mai muhimmanci.

    Ya bayyana cewa yayin ziyararsa a kauyen Faruruwa na karamar hukumar Shanono, ya ga sabbin hanyoyin kauyuka da gwamnati ke ginawa.

    A cewarsa, irin wannan gini zai taimaka wajen hanzarta amsa kai kan matsalolin tsaro ta hanyar inganta hanyoyin shiga yankunan da ke da nisa.

    Ya yi kira ga gwamna da ya tabbatar cewa kananan hukumomi na ci gaba da amfana da manyan ayyukan gina hanyoyi da za su hada su da sauran yankunan jihar yadda ya kamata.

    Sarkin ya tabbatar wa gwamna da cikakken goyon bayan majalisar masarautar Kano, tare da alkawarin ci gaba da aiki tare domin dawo da martabar Kano a matsayin cibiyar zaman lafiya, hadin kai da kasuwanci.

    Taron ya kunshi addu’o’i da karatun Alƙur’ani daga manyan malamai da mahardata daga dukkan kananan hukumomin jihar 44.

  • Gwamna Abba Ya yi Kira ga Jama’ar Kano Su ƙara Addu’a Kan Matsalar Tsaro

    Gwamna Abba Ya yi Kira ga Jama’ar Kano Su ƙara Addu’a Kan Matsalar Tsaro

    Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kira ga mazauna jihar da su ƙara tsananta addu’o’i domin samun zaman lafiya da kariyar Allah, sakamakon ƙalubalen tsaro da ke tasowa a jihar, ciki har da ƙaruwa a hare-haren ‘yan bindiga.

    Gwamnan ya yi wannan kiran ne a wani taron addu’a na musamman da gwamnatin jihar ta shirya, wanda aka gudanar a filin taro na Open Arena cikin fadar gwamnatin Kano.

    Gwamna Yusuf ya bayyana addu’a a matsayin “makami mafi ƙarfi wajen yakar sharrin mugaye da duk wanda ke neman cutar da bil’adama,” inda ya nanata muhimmancin hadin-kai a addu’a domin kare jihar.

    Ya roƙi malamai da shugabannin addini su ci gaba da jagorantar al’umma wajen yin addu’o’in neman zaman lafiya mai ɗorewa a Kano.

    Gwamnan ya nuna damuwa kan hare-haren ‘yan bindiga da aka samu a wasu yankuna na jihar kwanakin baya, yana mai cewa lamarin baƙon abu ne, kuma na buƙatar rokon Ubangiji domin kawo sauki.

    Ya bayyana cewa duk da cewa gwamnati na ƙoƙarin ƙarfafa matakan tsaro, addu’a dole ta taimaka wajen cike gibi tare da ƙarfafa waɗannan matakai.

    A nasa jawabin, Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga jama’a da su ƙara jajircewa wajen yin addu’a domin zaman lafiya, cigaba da haɗin kan Kano.

    Sarkin ya yaba wa gwamnatin jihar bisa tsara taron addu’ar, yana mai cewa babban abin bukata ne ganin halin da ake ciki na tsaro a wasu yankunan jihar.

    Taron addu’ar na musamman ya kunshi karatun Alƙur’ani da addu’o’i na musamman da manyan malamai daga sassa daban-daban suka jagoranta.

    Masu halarta sun roƙi rahamar Allah, kariya da shiriya domin kawo ƙarshen matsalolin tsaro tare da tabbatar da ci gaba a cikin Jihar Kano.

  • Dandazon Al’umma Sun Tarbi Shugaban Karamar Hukumar Rano Bayan Dawowarsa Aiki

    Dandazon Al’umma Sun Tarbi Shugaban Karamar Hukumar Rano Bayan Dawowarsa Aiki

    A karamar hukumar Rano ta Jihar Kano, al’umma daga sassa daban-daban sun yi tururuwa a safiyar yau domin tarbar shugaban karamar hukumar, Hon. Naziru Rano, wanda ya dawo bakin aiki bayan ɗan hutu.

    IMG 20251120 WA0032

    Tun kafin isowarsa, daruruwan maza da mata sun cika filin taro tare da rera wakoki da kwararo addu’o’i na fatan alheri. Wani bangare na jama’a ma sun bayyana cewa dadadden kishin ci gaba da shugabancin Hon. Naziru Rano ne ya sa suka fito kwansu da kwarkwata domin nuna goyon bayansu gare shi.

    IMG 20251120 WA0033

    Da yake jawabi bayan isowa, Hon. Naziru Rano ya gode wa al’ummar Rano bisa wannan tarba ta musamman da suka yi masa, yana mai tabbatar musu da cewa zai ci gaba da gudanar da ayyukan da suka shafi ci gaban al’umma da inganta rayuwar jama’a.

    IMG 20251120 WA0030

    Wasu daga cikin al’ummar da suka halarci taron sun bayyana farin cikinsu, suna cewa dawowarsa ya zo a lokacin da ake bukatar sa ido da sauri kan wasu muhimman shirye-shiryen da ake aiwatarwa a yankin.

    Taron ya gudana cikin natsuwa, inda aka rufe shi da addu’o’i na neman zaman lafiya, ci gaba, da samun nasara ga karamar hukumar Rano baki ɗaya.

  • Kano Online Media Chapel ta yabawa kamfanin Dala Food Nig da Kamfanin POP Cola

    Kano Online Media Chapel ta yabawa kamfanin Dala Food Nig da Kamfanin POP Cola

    Kungiyar yan jaridun yanar Gizo ta ƙasa reshen jihar kano, Online Media Chapel ta yabawa kamfanin Dala Food Nig limited da Kamfanin POP Cola, bisa irin girmamawa da karramawar da kamfanunuwa suka yiwa kungiyar, a yayin taron ƙarawa mambobinta ilimi da sanin makamar aiki da yadda za’a koyi amfani da fasahar AI (One Day Capacity Building).

    Shugaban kungiyar Abubakar Abdulkadir Dangambo ne ya bayyana haka, yayin gudanar da taron ranar Talata a ma aikatar sufuri ta jihar Kano.

    Kamfanin Dala Food Nig limited sun turo ma’aikatan su, inda suka dama kunun tsamiya aka rabawa mahalarta taron cikin girmamawa, manyan baƙi da kananan kowa ya yaba da kunun.

    Su kuma kamfanin POP Cola suma sun turo ma’aikatan su, inda suka kawo ruwa da lemuka kala-kala aka rabawa mahalarta wannan taro.

    Dangambo ya kara yabawa kamfanunuwan duba da yadda aka tura musu buƙatar hakan a kurenren lokaci, kuma suka amince suka zo wajen taron da kayayyakin nasu.

    A ƙarshe Abubakar Dangambo ya yi musu fatan alheri da kasuwa mai albarka cikin harkokin su.

  • Iyaye Sun Koka Kan Kuɗin Yaye Dalibai ₦750,000 a Jami’ar Maryam Abacha Kano

    Iyaye Sun Koka Kan Kuɗin Yaye Dalibai ₦750,000 a Jami’ar Maryam Abacha Kano

    Kungiyar iyayen dalibai masu karatu a Jami’ar Maryam Abacha da ke Kano sun nemi Hukumar Karɓar Korafe-korafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano da ta sanya baki kan ƙorafin da suka gabatar game da kuɗin shirye-shiryen bikin yaye dalibai da jami’ar ta ƙayyade, wanda ya kai naira dubu 750.

    Iyayen sun bayyana cewa adadin kuɗin ya yi tsauri matuƙa fiye da yadda ya dace, lamarin da ke haifar da nauyi mai yawa ga iyaye da masu kula da dalibai.

    Da yake magana da manema labarai, ɗaya daga cikin iyayen daliban, Alhaji Yusuf Muhammad, ya ce sun nemi agajin hukumar ne saboda ganin cewa kuɗin da aka saka bai yi daidai da yanayin tattalin arzikin da ake ciki ba. Ya ce abin ya jefa iyalai da dama cikin damuwa, saboda barazanar da jami’ar ta yi cewa duk dalibin da bai biya kuɗin ba ba za a bashi takardar kammala karatu ba.

    Haka kuma, Hajiya Fatima Itama, ɗaya daga cikin iyayen da yaransu za su kammala karatu, ta ce tsadar kuɗin ta sanya iyaye da dama cikin tashin hankali, inda wasu ke ganin hakan na iya hana ’ya’yansu samun takardar kammala karatu duk da wahalar da suka sha wajen biyan kudaden makaranta a tsawon shekaru.

    A nasa jawabin, shugaban Hukumar Karɓar Korafe-korafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Kano, Sa’idu Yahaya, ya tabbatar da cewa sun karɓi ƙorafin iyayen daliban, kuma hukumar za ta gudanar da bincike mai zurfi domin samar da adalci a tsakanin bangarorin da abin ya shafa.

    Ya ce hukumar za ta tattauna da shugabancin jami’ar domin jin ta bakinsu, tare da bincikar duk bayanan da suka shafi kuɗin da ake ƙorafi a kansa, domin tabbatar da cewa an bi ka’ida kuma ba a ɗora wa iyaye abin da ya wuce ƙarfin su ba.

  • Gwamnatin Tarayya ta ɗau alwashin ceto ɗalibai mata da aka sace a Kebbi

    Gwamnatin Tarayya ta ɗau alwashin ceto ɗalibai mata da aka sace a Kebbi

    Gwamnatin Tarayya ta bayyana damuwa matuƙa kan sace ɗalibai mata na Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata da ke Maga, a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu ta jihar Kebbi, tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa.

    A wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya fitar, gwamnati ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa kare rayukan ’yan ƙasa, musamman na ɗalibai, na daga cikin manyan nauyikan da gwamnatin tarayya ke ɗauka a matsayin wajibi.

    Gwamnatin ta yi Allah wadai da harin da maharan suka kai, wanda ya yi sanadiyyar kashe wasu jami’an makarantar tare da yin garkuwa da ɗaliban.

    Ministan ya ce an bai wa hukumomin tsaro da leƙen asiri umarni kai tsaye da su binciko inda ’yan makarantar suke, su ceto su lafiya, sannan su tabbatar da cewa masu laifin sun fuskanci hukunci. Ya ce gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an kammala wannan aiki.

    Ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya na ƙara ƙaimi wajen inganta tsaro a cikin gida, ciki har da sake fasalin rundunonin soja, ’yan sanda, da na leƙen asiri domin samar da martani cikin sauri da inganci ga duk wata barazana.

    Sanarwar ta kuma nuna cewa Najeriya na ƙara haɗin gwiwa da ƙasashen yankin ta hannun ECOWAS, Ƙungiyar Tarayyar Afirka, da Rundunar haɗin gwiwa ta ƙasa da ƙasa ta MNJTF, domin ƙarfafa tsaron iyakoki da karya ƙungiyoyin ta’addanci da masu garkuwa da mutane.

    Ministan ya yi kira ga ’yan ƙasa da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da bai wa hukumomin tsaro goyon baya.

  • Gwamnatin kano Ta Yi Kira Ga Jama’a Su Rika Duba Lafiyarsu Don Rigakafin Ciwon Siga

    Gwamnatin kano Ta Yi Kira Ga Jama’a Su Rika Duba Lafiyarsu Don Rigakafin Ciwon Siga

    Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci al’umma da su rika zuwa cibiyoyin lafiya akai-akai domin yin gwaje-gwajen lafiya don kare kansu daga kamuwa da cutar sikari, wadda mutane da dama ke fama da ita ba tare da sun sani ba.

    Yayin bikin Ranar Masu Fama da Cutar Siga ta Duniya da aka gudanar a yau, wanda aka yi masa taken “Ciwon Siga a Kowane Mataki na Rayuwa,” Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya jaddada muhimmancin gano cutar da wuri da yin gwajin lafiya lokaci-lokaci.

    A cewar kwamishinan, yawan mutanen da ke kamuwa da ciwon siga na ƙaruwa, kuma hakan na faruwa ne sakamakon rashin gano matsalar da wuri da kuma rashin zuwa yin gwaji. Ya ce gwamnati na ci gaba da inganta cibiyoyin kiwon lafiya domin sauƙaƙa wa jama’a samun damar yin gwaje-gwaje da kuma samun kulawa yadda ya kamata.

    Dakta Abubakar ya bayyana cewa ciwon siga na daga cikin manyan matsalolin lafiya da ke addabar jama’a, musamman idan ba a gano shi tun farko ba, domin hakan na jawo matsaloli da raɗaɗi ga masu fama da shi.

    Kwamishinan ya yi kira ga iyaye da matasa da su rungumi cin abinci mai kyau, tare da yin motsa jiki akai-akai, yana mai cewa waɗannan matakai na taka muhimmiyar rawa wajen rage haɗarin kamuwa da ciwon siga.

    Haka kuma, ya shawarci masu fama da cutar da su rika bin dukkan shawarwarin likitoci domin kula da lafiyarsu da kuma sarrafa cutar yadda ya kamata.

    Dakta Abubakar ya kara da cewa gwamnatin jihar Kano za ta ci gaba da wayar da kan jama’a game da hanyoyin kariya da kuma kula da masu fama da ciwon siga a fadin jihar.

    A ƙarshe, ya yi kira ga shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki da su mara wa gwamnati baya wajen fadakar da jama’a kan muhimmancin kula da lafiya da yin gwaje-gwaje lokaci-lokaci.