labarai

Gwamnan kano Ya Umurci kwamishinan Shari’a AG Maude da Ya Binciki Zargin Hari da Aka Yi wa Rabi Hamza Danladi Nasidi

Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya nuna matuƙar damuwa kan mummunan harin da Rabi Hamza Danladi Nasidi ta ce an kai mata, wanda ake zargin wani Kabiru Aminu ya aikata a gidanta. Rahotanni sun nuna cewa an ji mata mummunan rauni da wuka a bakinta, lamarin da ya hana ta cin abinci tare da jefa lafiyarta cikin halin ƙunci.

Duk da cewa an fara tura wanda ake zargi gidan yari ta kotun Majistare mai lamba 36 har zuwa ranar 20 ga Janairu, 2026, daga baya wanda abin ya shafa ta ga alamar an sake shi, abin da ya haifar da damuwa a tsakanin jama’a. A cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, Rabi Hamza Danladi Nasidi ta roƙi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya sa baki domin tabbatar da adalci.

Da zarar Gwamna Abba ya samu labarin faruwar lamarin, ya nuna damuwar sa kan taɓarɓaren yadda aka gudanar da shari’ar, tare da hanzarta umartar Babban Lauyan Jiha kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, da ya gudanar da cikakken bincike tare da ɗaukar duk matakan shari’a da suka dace.

Babban Lauyan Jiha ya tabbatar wa Gwamnan cewa za a gudanar da cikakken bincike, kuma duk wanda aka samu da hannu a lamarin za a ɗauki mataki a kan sa bisa tanadin doka.

Gwamnati ta jaddada kudurinta na kare ‘yancin jama’a, tabbatar da walwala da jin daɗin al’umma, da kuma tabbatar da adalci ba tare da tsoro ko son zuciya ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button