labarai

Bichi Teachers College Aji na 1980 Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai da Taimakon Juna

Kungiyar tsaffin dalibai ta Bichi Teachers College, aji na 1980, ta yi kira ga dukkan kungiyoyin ɗalibai da su ƙara maida hankali wajen tallafa wa junan su, musamman mambobin da ke cikin halin ƙaƙƙarfan rayuwa, domin ƙarfafa zumunci, haɗin kai da kuma bunƙasa jin daɗin al’umma baki ɗaya.

Shugaban ƙungiyar, Alhaji Danlami Muhammad Fagge, ne ya bayyana wannan kira yayin taron sadar da zumunci da ƙungiyar ta gudanar a yau Lahadi.

Ya bayyana cewa tallafawa juna na daga cikin muhimman manufofin ƙungiyar tsaffin dalibai, inda ya ce rashin kulawa da halin da wasu mambobi ke ciki kan iya kawo cikas ga zaman lafiya da ci gaban ƙungiya.

Alhaji Danlami ya jaddada cewa haɗin kai da taimakon juna su ne ginshiƙan da suka sa tsofaffin ɗalibai ke ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki ɗaya tun bayan kammala karatu.

Ya ce ƙungiyoyin tsaffin dalibai ba wai don haɗuwa kawai ake kafawa ba, har ila yau don tallafawa juna a lokutan ƙalubale kamar rashin aikin yi, matsalolin lafiya da kuma wasu buƙatun rayuwa.

Ya kuma yi kira ga mambobin ƙungiyar da su ƙara himma wajen bayar da gudummawa, domin kafa asusun tallafi na musamman da za a rika amfani da shi wajen taimaka wa marasa ƙarfi, gami da tallafawa harkokin ilimi da na zamantakewa a cikin al’umma.

A yayin taron, wasu daga cikin mambobin ƙungiyar sun bayyana ra’ayoyinsu, inda suka yabawa shugabannin ƙungiyar bisa ƙoƙarin da suke yi na ƙarfafa zumunci da haɗin kai.

Wasu mahalarta taron sun bayar da shawarwari kan hanyoyin bunƙasa ayyukan ƙungiyar, musamman wajen amfani da ilimi da ƙwarewar mambobi don tallafa wa matasa da ɗalibai masu tasowa.

Taron sadar da zumuncin ya samu halartar manyan tsaffin dalibai daga sassa daban-daban na ƙasar, inda aka yi addu’o’i na neman zaman lafiya da albarka, tare da ɗaukar wasu muhimman shawarwari da za su taimaka wajen ƙarfafa ayyukan ƙungiyar a nan gaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button