Majalisar Dokokin Kano Ta Gayyaci Shugaban SUBEB Kan Rashin Gamsuwa Da Daukar Ma’aikata

46368163 2277760032237103 6832991413987180544 n

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta gayyaci Shugaban Hukumar Ilimin Bai Ɗaya ta Jihar Kano (SUBEB) domin bayyana a gaban ta, biyo bayan nuna rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da ɗaukar ma’aikata da hukumar ta yi.

A yayin gabatar da kudiri kan batun, dan majalisar jiha mai wakiltar ƙaramar hukumar Danbatta, Murtala Musa Kore, ya bayyana damuwa kan yadda aka aiwatar da tsarin daukar aikin, inda ya buƙaci a sake duba lamarin domin tabbatar da adalci da bin ka’ida.

Majalisar ta ce za ta saurari bayanin hukumar SUBEB kafin yanke mataki kan matakin da ya dace a dauka.

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *