Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa Najeriya na daga cikin ƙasashen da ke kan gaba wajen yawan masu fama da cutar zazzabin cizon sauro, lamarin da ya sa ta ƙara ɗaukar matakan gaggawa domin daƙile yaduwar cutar a faɗin jihar.Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ƙasar nan na kan gaba a ƙasashen Afrika wajen yawan masu fama da cutar zazzabin cizon sauro, inda kano take da kaso 18 cikin 100 na masu fama na cutar, lamarin da ya sa gwamnatin ta ƙara ɗaukar matakan gaggawa domin daƙile yaduwar cutar a faɗin jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a wani ɓangare na bikin World Malaria Day. Ya ce gwamnatin jihar ta mayar da hankali wajen samar da magunguna, kayan gwaji da sauran muhimman kayan aikin kiwon lafiya domin ƙarfafa yaƙi da cutar.
A cewarsa, gwamnati na kuma ƙoƙarin inganta wayar da kan jama’a kan hanyoyin kariya daga cutar, musamman a yankunan karkara inda ake samun yawaitar sauro. Ya ƙara da cewa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen rage yawan masu kamuwa da cutar.
Dakta Abubakar Labaran Yusuf ya yi kira ga al’umma da su riƙa bin matakan kariya, ciki har da amfani da gidan sauro mai maganin kashe sauro, tsaftace muhalli, da kuma guje wa barin ruwa ya tsaya a wurare da sauro ke haihuwa.
Haka kuma ya jaddada cewa idan aka lura da alamomin cutar kamar zazzaɓi, ciwon kai da kasala, ya kamata a garzaya asibiti domin a yi gwaji da samun magani cikin gaggawa.
Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa zazzabin cizon sauro na daga cikin manyan cututtuka da ke kashe mutane a Najeriya, musamman yara ƙanana da mata masu juna biyu, don haka akwai buƙatar haɗin kai daga kowa wajen yaƙi da cutar.
Gwamnatin jihar ta kuma yi alƙawarin ci gaba da tallafawa cibiyoyin kiwon lafiya tare da samar da isassun kayayyaki domin tabbatar da cewa ana rage yaduwar cutar a fadin jihar Kano.
Have any thoughts?
Share your reaction or leave a quick response — we’d love to hear what you think!
