Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bisa samar da ingantaccen muhalli mai kyau ga masu zuba jari, tare da jaddada aniyar gwamnati na ƙara ƙaimi wajen buɗe ƙarin damammaki ga masu zuba jari na cikin gida da na ƙasashen waje.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya bayyana wannan yabo a wajen bikin buɗe wata babbar masana’antar sarrafa kayan gona ta AFCOTT GRAINS a Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar Kano, Mustapha Muhammad, ya fitar, dangane da Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Mataimakin Shugaban Ƙasar, wanda Ministan Noma da Tsaron Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya wakilta, ya bayyana cewa kamfanin da ke da ƙarfin sarrafa ton 40,000 na sesame da kuma ton 20,000 na sauran hatsi, ba wai kawai cibiyar sarrafa abinci ba ce, har ma tana ƙarfafa fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje, ƙara darajar amfanin gona, canja fasaha, ƙara kuɗaɗen shiga na manoma da kuma samar da ayyukan yi ga al’umma.
Ya kuma yaba wa kamfanin AFCOTT GRAINS ƙarƙashin rukunin kamfanonin Kewalram Chanrai Group bisa wannan gagarumin aiki.
Tun da fari, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa jihar Kano ta kasance abin koyi wajen samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari, kuma a koda yaushe tana buɗe ƙofofi ga harkokin kasuwanci.
Gwamnan, wanda Shugaban Ma’aikatansa, Dakta Suleiman Wali Sani (mni) ya wakilta, ya ce Kano na ci gaba da kasancewa ƙasa mai armashi ga zuba jari, musamman a fannin noma da sauran bangarori.
Ya ƙara da cewa Kano na da kusan hekta miliyan 1.8 na ƙasar noma, amma kashi 40% ne kawai ake amfani da shi, wanda hakan ya sa gwamnati ke ƙara himma wajen bunƙasa noma ta hanyar ƙarfafa amfani da injinan zamani, faɗaɗa hanyoyin ban ruwa da kuma inganta ayyukan masu ba da shawara ga manoma.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa an ɗauki ma’aikatan ba da shawara kan noma sama da 1,000, an sayo kayan aikin noma na zamani, tare da gina madatsun ruwa domin ƙarfafa ci gaban noma a jihar.
Jihar Kano na haɗa masu samar da kayayyaki, ‘yan kasuwa da masu saye, wanda hakan ya sa ta zama cibiyar kasuwanci da ke haɗa kasuwanni har zuwa ƙasashen Afirka ta Tsakiya.
Have any thoughts?
Share your reaction or leave a quick response — we’d love to hear what you think!
