Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunan Alhaji Murtala Sule Garo ga Majalisar Dokokin Jihar Kano domin tantancewa da amincewa da shi a matsayin Mataimakin Gwamna.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna, Mustapha Muhammad ya sanya wa hannu.
Naɗin ya yi daidai da sashe na 191(3) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 (da aka yi wa kwaskwarima), wanda ya bai wa Gwamna damar naɗa Mataimakin Gwamna idan gurbi ya samu.
Matsayin ya zama fanko ne bayan murabus ɗin da tsohon Mataimakin Gwamna, Abdussalam Gwarzo ya yi da kansa a ranar 27 ga Maris, 2026.
Bayan yin shawarwari masu faɗi da manyan masu ruwa da tsaki, Gwamnan ya buƙaci Majalisar Dokokin Jihar da ta amince da naɗin Garo.
Murtala Sule Garo mai shekaru 48 ƙwararren ɗan siyasa ne kuma mai gogewa a harkar gudanarwa, inda ya shafe sama da shekaru ashirin yana hidima a mukamai daban-daban na zaɓe da na naɗi.
Ya taɓa rike mukamin Sakataren Tsara Tsare-tsare na Jam’iyyarsa a Jihar Kano, Mai Ba Gwamna Shawara na Musamman, da kuma Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo da aka zaɓa.
Haka kuma ya taɓa zama Shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi (ALGON) a Kano, Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, da kuma ɗan takarar Mataimakin Gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2023.
Naɗin nasa na daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa shugabanci da tabbatar da ingantaccen aikin gwamnati a Jihar Kano.

