Jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya, wasu fusatattun Matasa sun kashe mutane uku ta hanyar ƙona su da ransu, bayan zargin su da hannu a kisan wani basarake a Ƙaramar Hukumar Langtang ta Arewa.
Inda ranka ta rawaito, Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, kwana guda bayan da aka kai hari gidan basaraken ƙauyen Ƙwallon, mai riƙe da sarautar Ponzi Kwallak, inda aka kashe shi a daren Alhamis.
Shaidu sun bayyana cewa waɗanda ake zargin sun sace babur da wayar basaraken bayan sun hallaka shi, abin da ya haddasa fushin al’ummar yankin suka shiga nemansu.
Majiyoyi sun ce an kama mutanen ne yayin da suke yunƙurin sayar da baburin da aka sace, inda daga bisani aka ce sun amsa laifin da ake zargin su da aikatawa.
Sai dai, duk da yunƙurin wasu mazauna yankin na miƙa su ga jami’an tsaro, wasu fusatattun matasa sun ƙwace su, tare da cinna musu wuta har lahira a kusa da Sakatariyar Ƙaramar Hukumar.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, rundunar ’yan sandan jihar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
Wannan al’amari na ƙara jaddada damuwar da ake da ita kan yadda wasu jama’a ke ɗaukar doka a hannunsu, a maimakon barin hukumomin tsaro su gudanar da bincike da hukuncin bisa doka
Have any thoughts?
Share your reaction or leave a quick response — we’d love to hear what you think!
