Gwamnatin Jihar Kebbi ta kaddamar da sabbin motoci 50 masu ɗaukar fasinjoji 18-18, domin inganta harkokin sufuri a cikin jihar da kuma wajen ta.
An ƙaddamar da motocin ne a sabon tashar mota ta zamani (Ultra-Modern Motor Park) da aka gina a Birnin Kebbi, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ƙasa da Tsare-tsaren Birane, Alhaji Hayatuddeen Bawa.
Da yake jawabi a wajen bikin, Bawa ya bayyana cewa shirin na da nufin magance ƙalubalen sufuri da al’umma ke fuskanta, musamman wajen tafiye-tafiye masu nisa. Ya kuma lura cewa a baya Kebbi ce kaɗai a yankin Arewa maso Yamma da ba ta da ingantaccen tsarin sufuri na jama’a.
Kwamishinan ya yaba da ƙoƙarin Gwamna Nasir Idris wajen saka jari a fannin sufuri da inganta motsin jama’a.
Ya kuma buƙaci waɗanda aka bai wa motocin da su yi amfani da su yadda ya kamata domin tabbatar da dorewar shirin, yana mai cewa za a iya ƙara samar da wasu motocin idan aka kula da su yadda ya dace.
Bawa ya shawarci direbobi da su riƙa aiki da ƙwarewa, su guji ɗaukar lodin da ya wuce kima, tuƙin ganganci da gudun wuce gona da iri, tare da kula da gyaran motocin yadda ya kamata.
A nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar Masu Motocin Sufuri ta Ƙasa (NATO) reshen jihar Kebbi, Alhaji Ali Aliyu, ya gode wa gwamnatin jihar bisa wannan shiri, yana mai bayyana shi a matsayin babban ci gaba wajen inganta harkokin sufuri a cikin jihar da ma wajen ta.
Shi ma Mataimakin Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) mai kula da ayyuka a jihar Kebbi, DCC Musa Danladi, ya bayyana cewa an tantance tare da horas da direbobin kafin a ba su motocin.
Ya ƙara da cewa an gargadi direbobin da su bi dokokin hanya da ƙa’idojin tuƙi domin tabbatar da lafiyar fasinjoji da sauran masu amfani da hanya.
Kaddamar da motocin na nuna wani muhimmin mataki da jihar ke ɗauka wajen bunƙasa harkokin sufuri da haɗa yankuna daban-daban.
Have any thoughts?
Share your reaction or leave a quick response — we’d love to hear what you think!
