Majalisar Dokokin Jihar Kano ta gudanar da zaman tantancewa ga Murtala Sule Garo domin naɗa shi a matsayin mataimakin gwamnan jihar, a wani muhimmin mataki na cike gurbin mataimakin gwamna.
Zaman tantancewar ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin wani kwamiti na musamman mai mambobi 12 da majalisar ta kafa, wanda mataimakin shugaban majalisar, Muhammad Bello, ya jagoranta. Kwamitin ya yi wa Murtala Sule Garo tambayoyi kan ƙwarewarsa, gogewarsa a harkokin mulki, da kuma irin gudunmawar da zai bayar wajen ci gaban jihar Kano idan aka tabbatar da shi.
A yayin zaman, an duba tarihin rayuwarsa, irin ayyukan da ya gudanar a baya, da kuma rawar da ya taka a harkokin siyasa da gudanarwa, musamman kasancewarsa tsohon kwamishina kuma ɗan siyasa mai tasiri a jihar.
Bayan kammala tantancewar da tattaunawar sirri, Murtala Sule Garo ya bayyana wa manema labarai cewa zai yi aiki kafada da kafada da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, domin tabbatar da aniyar gwamnati ta samar da ci gaba mai ɗorewa ga al’ummar jihar.
Ya jaddada cewa zai goyi bayan manufofin gwamnatin Kano musamman shirin “Kano First”, wanda ya ce yana da manufar fifita buƙatun al’ummar jihar da inganta rayuwarsu ta fuskar tattalin arziki, ilimi da walwalar jama’a.
Zaman tantancewar ya samu halartar manyan jiga-jigan siyasa da suka hada da sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Tudunwada da Doguwa, Abba Bichi, da kuma wasu tsofaffin shugabannin Majalisar Dokokin Jihar Kano, wadanda suka halarta domin nuna goyon baya da kuma shaida muhimmin matakin.
Ana sa ran majalisar za ta kammala duk wasu matakai na doka da suka dace kafin amincewa da naɗin Murtala Sule Garo a hukumance a matsayin mataimakin gwamnan jihar Kano.
Have any thoughts?
Share your reaction or leave a quick response — we’d love to hear what you think!
