Sanata Oluremi Tinubu Ta Kaddamar da Titin Lodge, Ta Kuma Kaddamar da Aikin Titin Sarkin Yaki

Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta jagoranci bude sabon titin Lodge Road da aka kammala tare da ƙaddamar da aikin gina Titin Sarkin Yaki a Sabon Gari na ƙaramar hukumar Fagge.

Da take jawabi a wajen taron, Sanata Oluremi Tinubu ta jaddada muhimmancin ababen more rayuwa a matsayin ginshiƙi na ci gaban tattalin arziki, haɗin kan al’umma da bunƙasar ƙasa.

Ta bayyana cewa ingantattun hanyoyi na taimakawa wajen sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kayayyaki, inganta tsaro, tare da ƙarfafa tattalin arzikin jiha da na ƙasa baki ɗaya.

Ta kuma jaddada buƙatar ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya, Jihohi da ƙananan hukumomi domin tabbatar da al’umma sun amfana da ayyukan da suke buƙata.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana ziyarar Uwargidan Shugaban Ƙasar a matsayin abin alfahari da farin ciki ga al’ummar Kano, tare da nuna hakan a matsayin alamar haɗin gwiwa da ake buƙata domin cimma manufofin ci gaba.

Ya kuma sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tallafawa duk wani shiri da zai kawo ci gaba,a fadin jihar.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakuna, masu ruwa da tsaki da ‘yan siyasa, wanda ke nuna haɗin kai wajen aiwatar da ayyukan da suka shafi jin daɗin jama’a da ci gaba mai ɗorewa.

Haka kuma, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta Najeriya, Barau I. Jibrin, mambobin Majalisar Wakilai, wakilan gwamnonin yankin Arewa maso Yamma, shugabannin jam’iyyar APC da sauran fitattun baki sun halarci taron.

Have any thoughts?

Share your reaction or leave a quick response — we’d love to hear what you think!

Related Articles

Leave a Comment